Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a daren jiya a babban zauren majalisar dinkin duniya da ke birnin New York, inda ya ce 'yan ta'addan da suke cikin kasar Syria an san kasashen da suka fito, kuman san kasashen da suke ba su kudi da makami da kuma bude musu hanyoyin da suke shiga cikin Iraki da Syria, ya ce idan ba kawo karshen wannan ba harin Amurka da kawayenta a Syria ba zai kawo karshen 'yan ta'adda ba.
Shugaba Hassan Rauhani ya ce tun kafin lokacin Iran ta gaya wa kasashen yammacin turai da ma wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya da suke ganin cewa za su yi amfani da 'yan ta'adda domin cimma manufarsu ta siyasa kan gwamnatin Syria da cewa wannan babban kure ne, domin kuwa wadannan 'yan ta'addan daga bisani ya juyo kansu, kuma shi ne abin da yake faruwa a halin yanzu. ABNA